Connect with us

News

Jihohi 20 Sun Ciyo Bashin Sama Da Naira Biliyan 458 Cikin Wata Shida

Published

on

Gwamnonin Najeriya

Akalla jihohin Najeriya kusan 20 ne suka ciyo bashin da darajarsa ta kai Naira biliyan 458 cikin rabin farkon shekarar 2025, kamar yadda wani binciken jaridar Punch ya nuna.

Rahoton ya bayyana cewa jihohi da dama sun koma ciwo sabbin basussuka duk da cewa sun samu karin kuɗaɗe daga gwamnatin tarayya a wannan shekara. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da nauyin biyan bashin waje ke ƙaruwa, musamman saboda raguwar darajar Naira a kasuwannin duniya.

Advertisement

Aƙalla Mutum Bakwai Ne Suka Rasu Bayan Da Wata Tirela Ta Murƙushe Motoci Biyu

Ga wasu daga cikin jihohin da suka fi ciwo bashin a wannan shekarar:

Zamfara: Naira biliyan 28

Advertisement

Katsina: Naira biliyan 20.7

Gombe: Naira biliyan 20.3

Advertisement

Jigawa: Naira biliyan 10.98

Binciken ya nuna cewa jihohin sun kashe akalla Naira biliyan 235.58 wajen biyan bashin waje a cikin rabin farkon shekarar 2025. Wannan ya nuna ƙarin kashi 68.4% idan aka kwatanta da Naira biliyan 139.92 da aka biya a lokacin daidai da shi a shekarar 2024.

Advertisement

Masana sun ce ƙarin bashin da ake biya cikin Dala ya nuna yadda matsin tattalin arziki ke ƙaruwa a jihohi saboda raguwar darajar Naira.

Bayanai daga Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) sun nuna cewa gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun raba kuɗaɗe har Naira tiriliyan 10.13 daga Majalisar Raba Kuɗi ta Ƙasa (FAAC) a rabin farkon shekarar 2025.

Advertisement

Jihohi sun samu kusan Naira tiriliyan 3.425, wanda ya nuna ƙarin kusan kashi 43% idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 2.396 da suka samu a rabin farkon shekarar 2024.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending