News
Kotu Ta Umarci A Kamo Soja Kan Zargin Kisan Jami’in KAROTA A Kano
Babbar Kotun Jihar Kano ta umarci rundunar sojoji da ke Bukavu Barracks da ta tabbatar da an gabatar da wani soja da ake zargi da hannu a kisan wani jami’in Hukumar KAROTA, bayan rashin bayyana a gaban kotu har sau hudu.
A zaman kotun da aka yi ranar Talata karkashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Mahmud, an ci gaba da sauraron karar da ake yi wa Lance Corporal Tunde Momodu, da Yakubu Abdussalam da kuma Sagiru Yusuf Bichi, kan zargin haɗa baki wajen aikata laifi da kuma kisan kai — zarge-zargen da dukkansu suka musanta.
Lauyan gwamnati mai gabatar da kara, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya roki kotu ta bayar da umarnin kamo sojan da bai halarci zaman kotun ba, domin a ci gaba da shari’ar cikin adalci da gaskiya.
Mai shari’a Aisha Mahmud ta amince da bukatar, inda ta umurci kwamandan rundunar sojoji a Bukavu Barracks da ya tabbatar da cewa an gabatar da sojan a zama na gaba. Kotun ta kuma sanya 5 ga watan Disamba, 2025 a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraron shari’ar.
Ana zargin wadanda ake kara da cewa sun kwashe marigayi Yahaya Idris Ismail, wani jami’in KAROTA, yayin da yake bakin aiki. Bayan nan, rahotanni sun nuna cewa ya bi motar da ake zargin tasu ce domin daukar wasu kaya, amma daga baya aka yi zargin an kashe shi, inda ake cewa an yi amfani da wuka kafin a jefar da gawarsa a karkashin wata gada a Kano.
Lamarin dai ya girgiza al’ummar jihar, yayin da kotu ta jaddada cewa za ta tabbatar an bi doka wajen gurfanar da duk wanda ake zargi da hannu a kisan.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News15 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
