News
Gwamna Abba Ya Gabatar Wa Majalisar Dokokin Kano Kasafin 2026 Na Naira Tiriyan 1 Da Biliyan 368
Gwamnatin Kano Abba Kabir Yusuf, ya gabatar wa da majalisar dokokin jihar kasafin kuɗin shekarar 2026.
Abba, ya gabatar da kasafin a safiyar yau Laraba, lokacin da ya halarci zaman majalisar wanda ya kai Naira triliyan 1 da biliyan 368.
Wannan shine karon farko da gwamnatin jihar Kano ta gabatar da kasafin kudin da ya kai Naira triliyan.
Ayyukan raya ƙasa zasu lakume Naira biliyan 934, 640, 032, 101.00, yayin da ayyukan yau da kullum zasu lashe Naira biliyan 433, 487, 897, 170.00.
A yayin gabatar da kasafin gwamna Abba, ya ce gwamnatin sa ta aiwatar da kaso 80 cikin 100 na alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zabe.
Advertisements
