News
Dan Majalisar Jiha Na Ungogo Aminu Sa’ad Ya Rasu
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Karamar Hukumar Ungogo, Aminu Sa’adu Ungogo, ya rasu a Kano.
Mai magana da yawun Majalisar Dokokin Jihar Kano, Kamaludeen Sani Shawai, ya tabbatar da rasuwar ɗan majalisar , inda ya ce marigayin ya kamu da gajeriyar rashin lafiya jim kaɗan bayan ya isa Majalisar Dokoki.
A cewar Shawai, an garzaya da Aminu Sa’adu zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa da yammacin ranar.
Ya ƙara da cewa za a gudanar da sallar jana’izar marigayin da misalin ƙarfe 6 na yamma a ranar Talata.
Rasuwar Aminu Sa’adu ta haifar da jimami a Majalisar Dokokin Jihar Kano da kuma Karamar Hukumar Ungogo, inda abokan aikinsa da ‘yan mazabarsa ke bayyana alhini kan rasuwar ɗan majalisar, wanda ya kasance mai wakiltar yankinsa a zauren majalisar jihar.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
