News
Yan Siyasar Arewa Da Malaman Addinin Arewa Da Sarakunan Arewa Su Ne Suka Sayar Da Arewa —Naja’atu Muhammad
Fitacciyar ’yar gwagwarmaya, Naja’atu Muhammad, ta zargi wasu ’yan siyasa, malaman addini da kuma sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya da cewa su ne suka gaza kare muradun yankin, lamarin da ta ce ya janyo koma-baya da tarin matsaloli a Arewa.
Naja’atu ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da DCL Hausa, inda ta yi tsokaci kan makomar Arewacin Najeriya.
Kungiyar Matasan APC Ta Yi Kira Ga Kwankwaso Da Gwamna Abba Su Dawo Jam’iyyar APC
A cewarta, duk da yawan jama’a da albarkatun da yankin ke da su, rashin jagoranci nagari daga masu ruwa da tsaki ya hana Arewa cin gajiyar damar da ke gabanta.
Ta ce yawancin ’yan siyasa sun mayar da hankali ne kan ribar kansu da ta jam’iyyunsu, maimakon su fifita walwalar al’umma.
Haka kuma, ta ce wasu malaman addini sun shiga siyasa ta hanyar da ke haifar da rarrabuwar kai, yayin da wasu sarakunan gargajiya suka kasa tsayawa tsayin daka wajen kare muradun jama’arsu.
A cewarta, “Arewa na da dukkan damar ci gaba, amma abin takaici, shugabanni da masu tasiri sun fifita kansu, suka bar talakawa cikin talauci, rashin tsaro da koma-baya.”
-
Uncategorized3 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News6 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
-
News2 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
