Connect with us

News

Idan Aka Dauki Kama Maduro A Matsayin Ba Komai Ba, Babu Kasar Da Ta Tsira —Dan Nicolas Maduro

Published

on

maduro large

Nicolas Ernesto Maduro Guerra, ɗan shugaban ƙasar Venezuela, Nicolás Maduro, ya yi kira ga ‘yan ƙasar su fito kan tituna don nuna adawa da kama mahaifinsa da matarsa, Cilia Flores, bayan an kwashi  su zuwa Amurka domin gurfanarwa a kotu.

Maduro Guerra, mai shekaru 35, wanda aka tuhuma tare da iyayensa a shekarar 2020 kan zarge-zargen hada-hadar miyagun ƙwayoyi , ya ce: “Za ku ga mu a kan tituna.”

Ya ƙara da cewa, “Za su ga cewa ba za mu nuna rauni ba. Na rantse da rayuwata, da mahaifina da Cilia, za mu fita daga wannan hali.”

Shugaban Venezuela da matarsa sun shiga hannun hukumomin Amurka a birnin New York, inda ake tuhumarsu kan laifukan tarayya. Maduro Guerra yana daga cikin jami’an ƙasar da har yanzu ake tuhuma a Venezuela kan zarge-zargen hada-hadar miyagun ƙwayoyi da sauran manyan laifuka.

Masu lura da al’amura sun ce kama Maduro zai iya kawo karin rikici a siyasance da tsaro a Venezuela, inda al’umma ke cike da fargaba.

 

Advertisement

CBC NEWS 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending