Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Bai Wa Polytechnics Damar Fara Bayar Da Shaidar Digiri ‎

Published

on

FB IMG 1762488671790 768x511

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce tana shirin bai wa manyan makarantun kimiyya da fasaha, wato Polytechnics, damar bayar da shaidar digiri, domin kawo sauyi a tsarin ilimi na ƙasar.

‎Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron bita da ya haɗa kwamishinonin ilimi na jihohi, shugabannin Makarantu da sauran manyan jami’an ilimi.

ZARGIN YUNƘURIN KIFAR DA GWAMNATI: Falana Ya Bukaci Sojoji Su Ba ’Yan Najeriya Haƙuri

‎A cewar ministan, gyaran dokar Polytechnics da ake yi a halin yanzu zai magance matsalar banbancin HND da digiri, wadda ta daɗe tana janyo ƙorafi daga masu karatun makarantun fasaha.

‎Dokta Alausa ya ce wannan mataki wani muhimmin sauyi ne a manufofin ilimi, wanda zai kawo ƙarshen shekaru da dama na nuna wariya ga masu takardun Polytechnics.

‎Ya ƙara da cewa sauyin ba zai rage ƙwarewar koyarwar aikace-aikace da Polytechnics ke da ita ba, illa ma zai ƙarfafa su tare da ɗaga matsayin shaidar karatun da suke bayarwa.

Advertisement

‎A cewarsa, ba wa Polytechnics damar bayar da digiri zai ƙara jawo haɗin gwiwa da masana’antu, da kuma ƙara amincewar jama’a da tsarin karatun su.

 

 

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending