News
Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Mutane Uku Kan Zargin Sayen Motar Miliyan 75 Da “Fake Alert” Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da sayen wata mota kirar Mercedes Benz GLE ta hanyar amfani da sakon tura kuɗi na bogi (fake alert), lamarin da ya janyo asarar kuɗi har naira miliyan saba’in da biyar (₦75,000,000).
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an kama mutanen ne a ranar 28 ga Janairu, 2026, a unguwar Kabuga da ke Kano.
NAPTIP Ta Kama Mutumin Da Ake Zargi Da Safarar Yara 10 A Jalingo
A cewar CSP Kiyawa, sunayen wadanda aka kama sun hada da Ibrahim Tijjani, Jamilu Auwal da Mohammed Nura Dauda.
Binciken farko na ’yan sanda ya nuna cewa mutanen sun sayi motar ne daga unguwar Gwarinpa da ke Abuja, bayan da aka tura sakon shaidar biyan kuɗi na bogi, wanda ake zargin wani Ibrahim Yahya ne ya aikata.
Ya ce tuni rundunar ta kwato motar, tare da mika ta ga Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) domin ci gaba da bincike da kuma gano duk wasu da ke da hannu a lamarin.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa jami’an rundunar bisa jajircewa da kwarewa wajen gano laifin, yana mai jaddada aniyar rundunar na dakile laifukan damfara da zamba ta zamani.
Haka kuma, CP Bakori ya bukaci jama’a da su kasance masu taka-tsantsan wajen mu’amalar kuɗi, musamman kan sakonnin tura kuɗi, tare da gaggauta kai rahoton duk wani motsi na zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa ko ta lambobin gaggawa na rundunar.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
