News
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kwato Alburusai 415 , Sun Kama Direba Da Fasinjoji A Akwa Ibom
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom ta sanar da kwato alburusai 415 daga wata motar haya da ke kan hanyar Calabar–Itu, tare da kama direba da wasu fasinjoji da ake zargi da hana jami’an tsaro gudanar da aikinsu.
Sanarwar da DSP Timfon John, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ta fitar, ta ce lamarin ya faru ne a ranar 23 ga Janairu, 2026, da misalin karfe 11 na dare, yayin da jami’an rundunar ke gudanar da aikin bincike na yau da kullum.
Masana Kiwon Lafiya Sun Nuna Damuwa Kan Karuwar Mutuwar Mata Masu Juna Biyu
Jami’an sun tsayar da motar mai lambar ARR600ZY, inda suka gano akwatin alburusai a cikinta.
Direban motar, Ikenna, ya musanta mallakar alburusan, yana mai cewa an ba shi su ne domin kai wa wani mutum da ba a bayyana sunansa ba a Calabar.
A yayin bincike, wani fasinja mai suna Excel ya yi ƙoƙarin hana jami’an ‘yan sanda gudanar da aikinsu, yayin da wani mai suna Bright, wanda ya yi ikirarin jami’i ne a Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), bai gabatar da sahihin shaidar aiki ba.
Bincike ya kuma kai ga kama Ndubisi Raphael, dan shekara 36, dan asalin kauyen Nyaje a Karamar Hukumar Akamkpa ta Jihar Cross River, a garin Calabar, wanda aka tsare domin ci gaba da bincike.
