News
Gobara Ta Tashi A Kasuwar Singa Da Ke Kano
Rahotanni na gaggawa sun tabbatar da cewa an samu tashin gobara a kasuwar Singa da ke Bello Road, cikin birnin Kano, lamarin da ya tayar da hankulan ’yan kasuwa da mazauna yankin.
Bayanan da Jaridar INDA RANKA ke samu sun nuna cewa gobarar ta tashi ne a safiyar yau, inda wutar ta fara cin wasu sassan kasuwar, lamarin da ya haddasa asarar kayayyaki da dukiyoyin ’yan kasuwa.
Gobara Ta Tashi A Kasuwar Singa Da Ke Kano
Wasu daga cikin mutanen da suka fara kai dauki a wajen sun shaida cewa ana matukar bukatar ɗaukin gaggawa, musamman daga jami’an kashe gobara, domin dakile yaduwar wutar da rage barnar da ake fuskanta.
Ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin gobarar ko asarar rayuka ba, yayin da jami’an tsaro da na agaji ke ci gaba da kokarin shawo kan lamarin.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
