Connect with us

News

Hisbah Ta Haramta Wa Mata Hawa Gefen Adaidaita Sahu A Kano

Published

on

Hukumar Hisbah Haramta Zancen Dare A Mota A Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kammala shirye-shirye domin fara aiwatar da dokar hana mata fasinjoji zama a gefen direbobin Adaidaita Sahu, domin inganta tarbiyya a cikin al’umma.

Auwalu Ado Sheshe, Daraktan Wayar da kai na Hukumar Hisbah ta Kano, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Juma’a.

Advertisement

INEC Ta Saka Ranar Zaɓen 2027 A Najeriya

Ya ce hukumar za ta gudanar da wannan aiki tare da hadin gwiwar kungiyar direbobin adaidaita sahu da masu su, domin tsaftace harkar sufuri da kuma kauce wa ayyukan da ka iya jawo fushin Allah (SWT).

Advertisement

A cewarsa, aikin zai mayar da hankali ne wajen hana mata zama kusa da direbobin wadanda ba su cikin maharamsu yayin zirga-zirga.

Ya kara da cewa hukumar ta umarci dukkan direbobin Adaidaita Sahu da su bi wannan doka domin kaucewa hukunci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending