Connect with us

News

Dakarun Sojin Amurka Sun Fara Sauka A Maiduguri

Published

on

FB IMG 1770201720847

Jiragen saman sojin Amurka sun fara sauka a birnin Maiduguri na jihar Borno, lamarin da ke nuni da fara wani sabon tsarin haɗin gwiwa na tsaro tsakanin Amurka da Najeriya.

Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito cewa wani jirgin sojin Amurka ya sauka da daren Alhamis a filin jirgin saman birnin da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Advertisement

Jami’an Hisbah Sun Kama Wadanda Suka Shirya Taron Casu Na Bankwana Da Shaidan A Kano 

Bayanai sun kuma nuna cewa ana sa ran sake saukar ƙarin wasu jiragen a ƙarshen mako a wani ɓangare na shirin aikewa da kusan dakarun sojin Amurka 200.

Advertisement

Jami’ai sun ce, jiragen na farko nau’in C-17 ne na jigilar kaya kuma suna ɗauke ne da manazarta bayanan sirri da masu ba da shawara da masu horaswa da kuma kayan aiki.

Jami’ai sun yi nuni da cewa waɗanɗa suka fara isa za su fi mayar da hankali ne kan kafa amintattun hanyoyin sadarwa tare da shirya tsarin tallafi na aiki tare da takwarorinsu na Najeriya.

Advertisement

Jami’an rundunar sojin Najeriya sun sha jaddada cewa sojojin Amurkan ba za su yi aiki a fagen daga ba.

 

Advertisement

BBC HAUSA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending