News
Yadda Mata Ke Daidaita Ibada Da Hidimar Iyali A Watan Ramadan
Kun taɓa tunanin yaya mata suke samun isasshen hutu da lokacin ibada da kuma kula da iyali a watan Ramadan?
A yayin da duk mai azumi yake fama da yunwa da ƙishirwa da ƙoƙarin ninka ayyukan ibada, haka su ma suke yi, amma kuma ayyukansu na kula da gida da girke-girke da sauransu ƙaruwa suke yi, musamman a lokacin buɗe-baki da sahur, da duk mai azumi ke shirin hutawa.
Ramadan wata ne na ibada, sadaukarwa da kuma farin ciki ga duk Musulmi.
Sai dai ga mata, musamman matan aure da matasa, yana zuwa musu da ƙarin gajiya da fargabar abubuwa da dama kamar aikin gida, cefane saboda hauhawar farashi, ko rashin kuɗi, da kuma makara sahur ko buɗe-baki. Ko yaya mata ma’aikata suke yi a irin wannan yanayi?
Malama A’isha Isyaku, na daga cikin mata ma’aikata da ke ƙare rayuwarsu ta watan Ramadan a wannan yanayi. Malamar makarantar sakandare ce kuma matar aure mai ’ya’ya huɗu. A wajenta, Ramadan ba wai kawai watan azumi ba ne, wata jarrabawa ce da kuma tsari da juriyar zuciya.
“A shekarun baya, ina jin tsoro idan Ramadan ya matso. Ba wai saboda wahalar azumin ba, sai dai saboda yadda zan daidaita komai ba tare da na rasa falalar watan ba. Ga aiki a makaranta, dawowa gida da gajiya, ga girki, ga kula da yara, sannan kuma uwa uba, ga ibada. Duk kuma babu wanda za a bari,” in ji ta.
Ta bayyana wa Jaridar Aminiya yadda a farkon aurenta kimanin shekaru 15 da suka gabata, take shiga Ramadan ba tare da wani tsari ba. A sakamakon haka, gajiya kan rinjaye ta, wani lokaci har ta rasa nutsuwa wajen ibada. Amma a hankali ta fahimci cewa ba Ramadan ke wahalar da ita ba, illa yadda take shiga cikinsa da fargaba.
Yanzu, kafin watan ya zo, A’isha tana tsara rayuwarta. Tana yin jadawalin abincin buɗe-baki da sahur, ta kuma kasafta kuɗin da take da shi, ta tsara lokacin aiki da na hutawa. Wannan tsarin na ba ta damar samun ɗan lokacin kanta, domin samun hutawa da kuma ibada—karatun Alqur’ani, zikiri da barci.
Abin da mata ke fargaba a Ramadan
Sai dai duk da haka, tsadar rayuwa ta sa wannan tsari ya zama mai wahala a shekarun baya-bayan nan.
Duk da cewa farashin kayan abinci a Kano ya yi ƙasa sosai fiye da yadda yake a shekarar da ta gabata, amma qarancin kuɗi a hannu ya sanya ba ta samu damar yin cefanen azumi yadda ta saba yi ba.
“Dubawa na yi na ga ɗan abin da nake samu a baya kamar ya fi na yanzu albarka. Samuna ya ƙaru, amma ba na iya yin rabin abin da nake yi a da. Kin ga dai Alhmadulillah kayan abinci sun yi sauƙi a bana ba kamar bara ba, amma wallahi shinkafa kwano biyar kawai na iya siya da taliya rabin katan da macaroni.
“Wake sai a cikin azumin ma zan iya sayen kwano biyu sai kuma na haɗa da gero kwano ɗaya. Iya abin da zan iya yi ke nan. Idan an yi sadaka mun samu to mun gode Allah. Idan ba a yi ba. haka za mu lallaɓa. Yunwa ce laifi.”
Aisha ta ce wannan ya sa mata da dama ke shiga Ramadan da fargaba. “Idan ba ki da kuɗi, za ki ji kamar kowace rana jarrabawa ce Ubangiji yake yi miki domin gwada imaninki.”
‘Kwanaki 10 na farko sun fi wahalar da ni’
Hajiya Tabawa Isa, mai shekaru 48 da ’ya’ya bakwai, cikakkiyar mai zaman gida ce. Ta fi shekuru 20 da yin aure. Ita ma ta ce duk da kasancewarta mazauniyar gida, watan Ramadan na ƙara mata aiki fiye da yadda take yi a sauran lokuta.
“Ni dama ba ni da aiki a waje, amma aikin gida ba ya ƙarewa.” in ji ta.
A lokacin sahur, ita ce ke tabbatar da kowa ya samu abinci kafin ta ci nata, haka ma a lokacin buɗe-baki, ita ce ke shirya komai, amma kuma ita ce mai cin abincin a ƙarshe bayan ta tabbatar kowa ya ƙoshi.
Bayan haka, tana kula da yara, ta tsaftace gida, ta kuma samu lokacin yin ibada.
A cewarta, abin da ya fi wahalar da ita shi ne tabbatar da komai ya tafi daidai a kwanaki goman farko na azumi.
“Wani lokaci kina so ki zauna ki karanta Alqur’ani,” ta ce, “amma yara na kuka, ko suna neman abinci. Ga ƙarancin barci. Ga maigida shi ma jira yake yi ki gama abin da za ki yi a kan lokaci. Idan kuwa kika sake kuka makara sahur ko buɗe-baki, to laifin a kanki zai ƙare.
“’Ya’yana duka maza ne, auta ta ce kaɗai mace. Don haka duk ficewa suke yi aiki su bar ni. Ni kaɗai ce dai nake yin komai. Kuma cikin hikimar Ubangiji ban taɓa gajiyawa ba. Sai abin da ba a rasa ba.”
Yadda na sama wa kaina sauƙi — Hajiya Tabawa
Duk da haka, Hajiya Tabawa ta ce Ramadan ba ya zo mata da ruɗani sosai kamar wasu matan. Dalili kuwa shi ne, ta ce yanzu ta ƙware da kuma sabawa da rayuwar gida. Ta san yadda za ta sauƙaƙa wa kanta aiki. Ba lallai sai girki mai wahala ba ko iri-iri ba. Ta jaddada cewa, “Abin da ake buƙata shi ne tsari da sauƙi.”
Wannan ra’ayi ya yi daidai da abin da Halimatu Abdullahi, ’yar jarida a Kano, ta bayyana. A cewarta, babban dalilin da ya sa mata suke fargaba idan Ramadan ya zo shi ne rashin tsari. “Wasu mata akwai su da ƙiwa. Wata har lokacin da ya kamata ta fara aiki ya yi ya wuce ba ta tashi ba. Sai ayyuka su taru su rincave..”
A irin wannan yanayin a cewarta, mace na shiga Ramadan da damuwa a zuciyarsu.
“Akwai kuma matsalar yin girki fiye da ƙima. Wasu matan suna dafa abubuwa da yawa, fiye da abin da za a iya cinyewa. Wannan yana ƙara gajiya da ɓarnar abinci.”
Halimatu ta kuma ce idan mace ta tsara rayuwarta, Ramadan yana zama mai sauƙi. “Idan har za a tsara komai, kafin a sha ruwa mace ta kammala ayyukanta, ta gyara kicin, har ta sami damar hutawa.”
Ta ce akwai mata da ke kammala girkin sahur tare da na buɗe-baki domin samun sauƙimn yawan ɗora sanwa da asuba. Wasu kuma suna adana abincin ta hanyoyin zamani. Wannan tsarin na ba su damar samun lokaci na ibada ba tare da gajiya ba.
Rayuwar mata ’yan boko a Ramadan
Ta kuma taɓo batun rayuwar mata ’yan boko a Ramadan. A cewarta, ba ilimin boko ne ke sauya mace ba, illa yadda take tsara rayuwarta.
“Yawancin mata masu aiki a waje suna da jadawalin aiki, kuma wannan yana taimaka musu wajen tsara sauran bangarorin rayuwa.”
Aisha Isyaku ta amince da wannan ra’ayi. Ta ce aikin koyarwa ya koya mata sanin darajar lokaci. “Idan ba ki tsara lokacinki ba, zai cinye ki.”
Amma ga matan da ba su yi boko ba, ko kuma ba su fita aiki, Ramadan ma na iya zama mai sauƙi idan an samu tsari. Hajiya Tabawa ta ce ba ta ga dalilin da zai sanya mace mai zaman gida ta shiga Ramadan da ruɗani ba. “Ai dama a gida kike. Idan kin san abin da kike yi, komai zai tafi daidai,” in ji ta.
Abin da mata suka fi so a Ramadan
Duk da haka, ta yarda cewa tsadar rayuwa da yawan yara na iya sa al’amura su yi wahala.
Duk da waɗannan ƙalubalen, akwai abubuwan da mata suka fi so game da Ramadan. Aisha da Hajiya Tabawa sun ambaci ƙaruwar ibada. Ramadan yana ba su damar kusantar Allah fiye da sauran lokuta.
Halimatu ta ce tana jin farin ciki da natsuwa a Ramadan fiye da kowane lokaci na shekara.
“Lada na ƙaruwa, ibada na ƙaruwa.” Wannan jin daɗin ne ke sa mata da dama su manta da wahalar.
Batun abincin buɗe baki da sahur ma yana da muhimmanci a rayuwar mata. A da, ana ɗaukar sahur a matsayin babban aiki, saboda tashi da tsakar dare, a yi girki. Amma yanzu, abubuwa sun sauya.
Yawancin mata suna haɗa shan ruwa da buɗe-baki kawai. Wasu suna adana abinci su dumama da sahur.
Wannan canji ya zo ne sakamakon canjin rayuwa da kuma tsadar kayan abinci.
Halimatu ta ce, “Yanzu an daina tashi da wurin ƙarfe biyun dare kamar yadda iyayenmu suke yi.” Wannan sauƙi yana taimaka wa mata su samu ƙarin hutu.
A gefe guda kuma, Ramadan yana qara haɗin kai a cikin gida. Duk da wahala, lokacin buɗe-baki iyali na taruwa a wuri ɗaya a ci a sha.
Aisha ta ce wannan lokaci ne da take jin daɗin kasancewa tare da ’ya’yanta da mai gidan kansa.
Hajiya Tabawa ta ce yana koya wa yara haƙuri da juriyar yunwa. Wannan ya sa take jin cewa dukkan gajiyarsu ba a banza suke yin ta ba.
