Connect with us

News

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Garin Maƙarfi A Jihar Kaduna

Published

on

Rahotanni da ke shigowa Jaridar Inda Ranka sun nuna cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin Maƙarfi da ke Jihar Kaduna a daren yau.

Majiyoyi daga cikin mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun shiga garin ne cikin dare, inda suka fara harbe-harbe da bindigogi wanda ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tashin hankali.

Advertisement

Mojtaba Khamenei Ya Gaji Mahaifinsa A Matsayin Jagoran Addinin Iran

Mazauna garin sun ce ana ci gaba da jin ƙarar harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya sa mutane da dama suka shiga gidajensu domin neman mafaka.

Advertisement

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu cikakken bayani kan ko akwai asarar rayuka ko dukiyoyi sakamakon harin.

Haka kuma ba a samu wata sanarwa daga jami’an tsaro ba dangane da lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending