News
“Siyasar Da Ba Ta Da Adawa Ba Dimokuraɗiyya Ba Ce” — Comrade Salisu Gambo Ditol Ya Soki Yawaitar Sauya Sheƙar ‘Yan Siyasa
Fitaccen ɗan gwagwarmayar al’umma, Comrade Salisu Gambo Ditol, ya bayyana cewa siyasar da ba ta da ƙarfi a bangaren adawa ba za a iya kiranta cikakkiyar dimokuraɗiyya ba.
Ditol ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan yadda wasu ‘yan siyasa a Najeriya ke ta sauya sheƙa daga jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar da ke mulki ba tare da tuntubar jama’ar da suka zaɓe su ba.
Dakarun Soji Sun Dakile Hare-haren Da Mayakan ISWAP Suka Kai Sansanonin Sojoji 5 A Borno
A cewarsa, zuwa yanzu akwai gwamnonin jihohi sama da talatin da suke karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), kuma mafi yawan sauya sheƙar da ake gani a siyasar ƙasar na faruwa ne daga wasu jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar mai mulki.
Ya ce abin da ke damun al’umma shi ne yadda wasu ‘yan siyasa da aka zaɓa a ƙarƙashin ƙananan jam’iyyu ke sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya ba tare da neman shawara ko yardar mutanen da suka zaɓe su ba.
“Sauya shugabanci cikin adalci da bin tsarin doka shi ne ginshikin cigaban dimokuraɗiyya. Amma sauya jam’iyya don biyan bukatar kai ko neman kariya ta siyasa ba shi ne cigaban da al’umma ke bukata ba,” in ji Ditol.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu wasu ‘yan siyasa sun fi fifita muradunsu na kashin kai fiye da bukatun jama’a, lamarin da ya ce yana raunana tubalin dimokuraɗiyya a ƙasar.
A cewarsa, wajibi ne al’umma su kasance cikin faɗakarwa tare da fahimtar cewa irin wadannan matakai na sauya sheƙa ba tare da la’akari da ra’ayin masu zaɓe ba ba su dace da ruhin dimokuraɗiyya ba.
Ditol ya bukaci ‘yan Najeriya su riƙa bibiyar ayyukan shugabanni tare da tabbatar da cewa siyasa ta ci gaba da tafiya a kan turbar gaskiya, adalci da kuma hidima ga al’umma.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
