Connect with us

News

Ydda Mutane Suka Je Ɗiban Ganima Bayan Faɗuwar Tankar Man Fetur A Ibadan

Published

on

Screenshot 2026 03 22 at 22.10.45

wani sabon bidiyo ya sake nuna yadda wasu mutane ke ci gaba da jefa rayukansu cikin hadari yayin da suke kwasar man fetur daga tankar da ta yi hatsari.

RahotanniRahotanni daga birnin Ibadan sun ce wasu mazauna yankin sun taru a kan titin Academy zuwa Iwo Road, inda wata tankar mai ta kife, suka fara dibar man fetur duk da barazanar tashin gobara ko fashewa.

Wata Mata Ta Haifi ’Yan Huɗu Lokaci Guda A Ogun

Bidiyon da aka wallafa a ranar Lahadi ya nuna jama’a na cika galan da kwantena da mai, ba tare da la’akari da hadarin da ke tattare da irin wannan aiki ba.

Hukumomi sun dade suna gargadi kan wannan dabi’a, wadda ke yawan janyo asarar rayuka a fadin Najeriya.

A cewar Hukumar  FRSC akalla mutane 411 ne suka mutu a shekarar 2024 sakamakon irin wadannan lamurra.

Advertisement

Ko a farkon shekarar 2026 ma, an sake samun irin wannan lamari a yankin Apapa, inda wata tankar dizal ta kife, jama’a suka fara kwasar mai kafin jami’an agaji su iso wurin.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Legas ta gargadi al’umma da su guji kusantar tankunan da suka yi hatsari, tana mai cewa hakan na iya haddasa mummunar gobara cikin gaggawa.

Hukumomi na ci gaba da jan hankalin ‘yan Najeriya da su fifita tsaron rayukansu, suna mai jaddada cewa neman riba ta wucin gadi bai kamata ya kai ga rasa rai ba.

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending