News
Kotu Ta Tura Ma’aurata Kurkuku Tsawon Shekaru 15 Bisa Laifin Sayar Da Jarirai
Hukumar da ke yaki da fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) reshen jihar Cross River ta sanar da samun nasarar hukunta wasu ma’aurata da kotu ta yanke musu hukuncin dauri bisa laifin safarar jarirai.
Ma’auratan, Esther Ini Udo da mijinta Eyo Stephen Udo, sun fuskanci tuhume-tuhume guda hudu da suka shafi saye da sayar da jarirai domin cin moriya, wanda ya saba da dokar hana fataucin mutane ta shekarar 2015.
A cewar bayanan da aka gabatar a gaban kotun tarayya da ke Calabar, matar ta sayar da jaririnta da ta haifa kan kudi Naira dubu 300 ga wata mai suna Oluchi Judith, wadda jami’ai ke nema ruwa a jallo.
Haka kuma, an bayyana cewa ma’auratan sun sayi wani yaro mai shekara guda kan Naira dubu 150 daga wasu mutane biyu, sannan suka sake sayar da shi kan Naira dubu 400 ga wannan mata.
Kotun ta nuna matukar damuwa kan wannan aiki, tana mai jaddada cewa safarar jarirai babban laifi ne da ke tauye hakkin bil’adama.
Duk da cewa wadanda ake tuhuma sun musanta zargin a farko, kotun ta same su da laifi a kan dukkan tuhume-tuhumen da aka gabatar musu.
Mai shari’a I. Ojukwu ya yanke wa kowannensu hukuncin daurin shekaru 15 tare da tarar Naira miliyan biyu, inda aka ce hukuncin zai fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, 2026.
Haka zalika, kotun ta umarci NAPTIP da ta kamo Oluchi Judith domin gurfanar da ita a gaban kotu bisa zargin hannu a wasu laifukan fataucin mutane.
