Connect with us

Sports

NPFL: An Ci Tarar Kano Pillars Naira Miliyan 15

Published

on

KANO

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta fuskanci hukunci daga mahukuntan NPFL bayan wasu abubuwa da suka faru a wasan da ta karɓi bakuncin Rivers United a ranar Lahadi, 19 ga Afrilu, 2026.

Mahukuntan gasar sun ce ƙungiyar ta kasa samar da ingantaccen tsaro a filin wasa, abin da ya bai wa wasu mutane damar shiga wuraren da aka hana. Sun ƙara da cewa lamarin ya jefa lafiyar ‘yan wasa da jami’an wasa cikin haɗari.

Advertisement

JAMB Ta Fitar Da Sakamakon jarabawar UTME Na Ranar Litinin

Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu magoya bayan ƙungiyar sun shiga cikin filin wasa ba tare da izini ba, tare da aikata halaye da suka haɗa da cin zarafi da tsoratar da jami’an wasa, lamarin da ya saba wa ƙa’idojin gasar.

Advertisement

Hukuncin da aka yanke

Sakamakon haka, an ci tarar ƙungiyar kamar haka:

Advertisement

Naira miliyan 4 saboda rashin isasshen tsaro

Naira miliyan 3 kan halaye marasa kyau da suka bata sunan wasa

Advertisement

Naira miliyan 3 kan rashin kula da magoya baya

Naira miliyan 3 kan cin zarafi da tsoratar da yan wasa

Advertisement

Naira miliyan 2 kan haddasa tsaiko da katsewar wasa

Jimillar kuɗin ya kai Naira miliyan 15.

Advertisement

Baya ga tara, an kuma umarci Kano Pillars da ta buga wasanni uku na gaba a gida ba tare da ‘yan kallo ba. Daya daga cikin wasannin zai gudana a wannan kakar, yayin da sauran biyun za su kasance a farkon kakar wasa mai zuwa.

Mahukuntan gasar sun ce ƙungiyar na da damar ɗaukaka ƙara cikin awanni 48 daga sanar da hukuncin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending