News
Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka Tarin ‘Yan-Ta’adda A Dajin Sambisa
Wani hari da rundunar sojin sama ta Nijeriya, NAF ya halaka tarin ’yanta’adda a dajin Sambisa da ke yankin arewa masu gabashin kasar, inda yake da sansanonin ƙungiyoyin ta’adda.
Wata sanarwa daga daraktan yaɗa labarai na hedikwatar Sojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodamet, ta ce harin ya faru ne a wani sashe da ake kira Yuwe da ke dajin na Sambisa .
Gwamantin Tarraya Ta Fitar Da Litar Man Jirgi Fiye Da Biliyan 1 Zuwa Turai Cikin Kwanaki 50
Sanarwar da aka fitar ranar talata, 21 ga Afrilun 2026, ta ambaci cewa harin ya yi “nasarar kawar da tarin mayaƙan da ke ɓuya a sashen Yuwe na Dajin Sambisa, kuma ya biyo bayan zafafa hari kan gungun ‘yanta’adda”
“Farmakin ya biyo bayan ƙwararan bayanan sirri, da sintirin soji da tattara bayanai da suka tabbatar da kasancewar gungun ‘yanta’adda da ke cikin ganuwa da maɓoya”, in ji sanarwar.
Ejodamet ya ƙara da cewa, “Cigaba da kai hare-hare ta sama yana haifar da kawar da sansanonin ‘yanta’adda, wanda ke tasiri wajen bayyana inda ‘yanta’addar suke”.
Rahotanni a watannin baya-bayan nan sun nuna cewa Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta samu nasarar kai hare-hare a yankunan arewa maso gabashin Nijeriya, ciki har da Azir da Musarram a jihar Borno.
Sakamakon wancan harin, bayanai sun tabbatar da kashe ‘yanta’ada 40.
Rundunar ta NAF ta jaddada cewa hare-haren da take kai wa na cikin shirin sojin na Operation Hadin Kai.
