Connect with us

News

Dakarun Sojin Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda A Kukareta, Sun Kashe 24

Published

on

WhatsApp Image 2026 04 23 at 10.56.31

Rundunar haɗin gwiwar sojin Najeriya ta Operation Hadin Kai (OPHK) ta ce ta dakile wani hari da ’yan ta’adda suka kai a yankin Kukareta da ke Arewa maso Gabashin ƙasar , inda ta kashe aƙalla mutum 24 a yayin artabun.

A ikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar 23 ga watan Afrilu 2026, ya ce harin ya faru ne a daren Laraba zuwa wayewar Alhamis, lokacin da maharan suka kai farmaki da nufin tayar da zaune tsaye.

Advertisement

Kwankwasiyya Ta Yi Allah-wadai Da Kalaman Da Asari Dokubo Ya Yi Kan Kwankwaso

Sai dai ya ce dakarun sojin sun mayar da martani cikin gaggawa, abin da ya tilasta wa ’yan ta’addan janyewa bayan sun yi asara mai yawa.

Advertisement

Sanarwar ta ƙara da cewa, bayan fafatawar, sojoji sun kwato makamai da dama da suka haɗa da bindigogi kirar AK-47 guda 18, manyan bindigogi na GPMG guda uku, da kuma wasu makamai masu linzami da harsasai.

Rundunar ta ce sojoji biyu sun samu raunuka a yayin artabun, amma an kai su asibiti kuma suna cikin yanayi mai kyau.

Advertisement

Haka kuma, ta bayyana cewa dakarun na ci gaba da bin sawun waɗanda suka tsere, inda aka gano alamun jini da wasu kayan agaji a hanyoyin da suka bi.

RundunarRundunar Operation Hadin Kai ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kai farmaki kan ’yan ta’adda a yankin, tana mai cewa za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomi domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending