Connect with us

News

Kano: Fitaccen Ɗan Kasuwar Man Fetur, Audu Manager, Ya Rasu Yana Da Shekaru 68

Published

on

1780525471994

Rahotanni sun bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwar man fetur kuma hamshaƙin mai zuba jari a harkar gidaje da kadarori a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ahmad, wanda aka fi sani da Audu Manager.

Ɗa ga marigayin mai suna Surajo Audu Manager, ne ya tabbatar da rasuwar mahaifin nasa ga jaridar Daily Nigerian, inda ya bayyana cewa ya rasu ne a yau Laraba a wani Asibiti mai suna Saudi German Hospital Cairo da ke birnin Cairo bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Advertisement

Wani Mutum Ya Rasa Ransa Wajen Dauko Wata Waya Da Ta Fada Rijiya A Kano

Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƴan kasuwa a Jihar Kano, inda ya yi fice a harkokin kasuwancin man fetur da kuma zuba jari a fannin gidaje. Rasuwarsa ta jawo alhini a tsakanin ‘yan kasuwa, abokai da masu hulɗa da shi a faɗin ƙasar nan.

Advertisement

Ana sa ran za a sanar da shirye-shiryen jana’izarsa daga iyalansa nan gaba kaɗan.

Allah Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa, Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa.. Amin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending