Connect with us

News

“Rahoton ‘The Historica Nigeria’ Ya Jawo Matakin Gwamnati yayin Da Aka Dakatar Da Sare Bishiyoyi A ARTV

Published

on

1780620107518

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da duk wani aikin sare bishiyoyi da ake yi a harabar tashar talabijin ta Abubakar Rimi Television (ARTV), bayan rahoton bincike da jaridar The Historica Nigeria ta wallafa kan zarge-zargen sare bishiyoyi da kuma damuwar mazauna yankin Hotoro da kewaye.

Umarnin ya fito ne daga Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, yayin wata ziyarar bazata da ya kai tashar domin duba halin da ake ciki.

Advertisement

RATTAWU Ta Yaba Wa Sunusi Bature Kan Gyaran Motar Ƙungiyar A Kano

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na ma’aikatar, Ameen Kabeer Yassar, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa Kwamishinan ya nuna matuƙar damuwa kan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, wanda ke nuna yadda ake sare bishiyoyi a harabar tashar, lamarin da rahoton The Historica Nigeria ya fito da shi fili.

Advertisement

Sanarwar ta ce Kwamishinan ya bayar da umarnin cewa daga yanzu babu wata bishiya da za a sare a harabar ARTV sai an samu sahalewar hukumomin da ke kula da harkokin muhalli da gandun daji.

Ya jaddada muhimmancin kare muhalli da kiyaye bishiyoyi, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani aiki da zai iya haifar da illa ga muhalli ba.

Advertisement

Baya ga batun sare bishiyoyi, Kwamared Waiya ya nuna rashin gamsuwarsa kan yadda ayyukan tashar suka ragu a ‘yan shekarun nan, inda ya bayyana cewa ARTV na bukatar cikakken garambawul domin ta dace da bukatun zamani.

Ya ce akwai bukatar sabunta kayan aiki, ƙara wa ma’aikata ƙwarewa ta hanyar horaswa, da kuma rungumar sabbin fasahohin yaɗa labarai domin tashar ta samu damar gogayya da sauran gidajen talabijin na zamani a faɗin ƙasar nan.

Advertisement

Kwamishinan ya kuma tabbatar da aniyar gwamnatin jihar na farfaɗo da tashar tare da mayar da ita ɗaya daga cikin manyan kafafen yaɗa labarai masu tasiri a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending