News
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
Hukumar ICPC ta yi gargaɗin cewa duk wani ma’aikaci ko cibiyar rajistar Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) da aka samu da laifin yi wa baƙi rajista a matsayin ’yan Najeriya, na iya fuskantar hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai kan harkokin tsaro da Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC) ta shirya wa masu gudanar da rajistar NIN a Abuja, tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro da sauran hukumomin tsaro.
Kofar Sulhu Ga Tubabbun ‘Yan Bindiga A Bude Take — Gwamna Radda
Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Darakta a ICPC, Mark Faison, ya ce duk wanda ya yi amfani da damar da aka ba shi wajen rajistar ’yan Najeriya ta hanyar da ba ta dace ba, ya karya amana kuma ya aikata laifin cin hanci.
Ya ce, “An ba ku damar yin rajistar ’yan Najeriya ne a madadin NIMC. Idan kuka yi amfani da wannan dama ba bisa ƙa’ida ba, kun ci amanar da aka ɗora muku, kuma doka za ta hukunta ku idan aka kama ku.”
Faison ya ƙara da cewa hukuncin irin wannan laifi shi ne daurin shekaru bakwai a gidan yari, yana mai kira ga masu rajistar da su taka rawarsu wajen kare tsaron ƙasa.
Jami’in na ICPC ya bayyana damuwa kan yadda wasu cibiyoyin rajista ke yi wa baƙi rajista a matsayin ’yan Najeriya, yana mai cewa hakan na haifar da babbar barazana ga tsaron ƙasa.
A cewarsa, jami’an shige da fice sun kama wasu mutane da aka ba su shaidar zama ’yan Najeriya ta hanyar rajistar NIN, amma daga bisani bincike ya tabbatar da cewa ba ’yan ƙasar ba ne.
Ya ce ICPC za ta ci gaba da sanya ido kan cibiyoyin rajista domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana a tsarin tattara bayanan ’yan ƙasa.
A nata ɓangaren, Babbar Darakta Janar ta NIMC, Abisoye Coker-Odusote, ta ce yayin da tsarin shaidar dijital ke ƙara faɗaɗa a fannoni daban-daban na rayuwa, buƙatar ƙarfafa tsaro da kare bayanan jama’a ta zama wajibi.
Ta gargaɗi masu gudanar da rajista da kada su yi amfani da wata manhaja ko tsarin aiki da NIMC ba ta amince da shi ba, tana mai cewa duk wani saɓani da ƙa’idojin tsaro na iya jefa tsarin shaidar ƙasa cikin haɗari.
Coker-Odusote ta kuma bayyana cewa hukumar za ta ƙara yawan bincike da sa ido kan cibiyoyin rajista domin tabbatar da bin dokokin kariyar bayanai da tsaron intanet.
Tun da farko, Shugaban Sashen Fasahar Bayanai da Shaidar Ɗan Ƙasa na NIMC, Suleiman Falade, ya ce ingancin bayanan da ake tattarawa shi ne ginshiƙin ingantaccen tsarin shaidar ƙasa.
