Connect with us

News

Akwai Yiwuwar Ƙara Kuɗin Kiran Waya Da Aika Saƙo A Najeriya 

Published

on

images

Hukumar kula da sadarwa ta Najeriya ta fara nazari akan kuɗaɗen da ake biya wajen kira da aikewa da saƙonnin kar-ta-kwana a ƙasar, shekaru 8 bayan da aka ƙara kuɗin.

Da yake jawabi a wurin taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki kan kayyadewa da daidaita farashin sada abokan hulɗa masu amfani da layukan lamfanoni mabanbanta na wayoyin salula, wanda aka gudanar a Lagos a wannan Talata, wani babban jami’i a kamfanin KPMG, Wole Adenekan, ya ce idan farashin ya yi kasa sosai, ba zai nuna ainihin kudin da ake kashewa wajen samar da hidimar sadarwar ba, kuma zai iya kashe ƙwarin gwiwar masu zuba jari a ɓangaren samar da ababen more rayuwa.

Advertisement

Gwamnatin Tarrayya Ta Musanta Shirin Soke NBAIS

Adenakan ya kuma ƙara da cewa hukumar kula da sadarwa ta Najeriya na sake nazari akan wannan farashi da zummar yin abin da ya dace.

Advertisement

Farashin jona sadarwa ko kuma Mobile Termination Rate, shi ne farashin da kamfanin sadarwa ke biyan wani kamfanin yayin da abokin cinikinsa ya yi kira kuma aka karɓa a wata hanyar sadarwa ta daban.

Shi ne tsarin farashin da ke haɗa kowane mai amfani da layin wayar hannu na Najeriya, ba tare da la’akari da kamfanin sadarwarsa ba, ko kuma wane abokin hulɗa ne ke kira ba.

Advertisement

A yanzu farashin da ake caji ya kai ₦3.90 a kowane minti guda zuwa ₦4.70.

Idan har aka sake ƙara farashin a nan gaba, masu amfani da wayoyin sadarwa a ƙasar za su biya ƙarin kuɗi don yin kira da aikewa da saƙon kar-ta-kwana wato SMS.

Advertisement

 

 

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending