Connect with us

News

Yadda Wata Budurwa Ta Hallaka Kanta Bayan Rabuwa Da Saurayin Da Ta Dade Tana Soyayya Da Shi

Published

on

Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra ta ce ta gano gawar wata budurwa mai shekaru 25 a garin Onitsha, lamarin da ake zargin ya kasance sakamakon hallaka kai bayan samun matsala a dangantakarta da saurayinta.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya fitar, ya bayyana cewa an tsinci gawar budurwar ne a ranar Alhamis, yayin da wasu bayanai da aka samu a wurin suka sa ake zargin cewa ta kashe kanta.

Advertisement

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

A cewar rundunar, wata wasika da ake zargin marigayiyar ta bari ta nuna cewa ta shafe lokaci mai tsawo tana soyayya da wani matashi mai suna Chigozie, kafin daga bisani ya sanar da ita cewa dangantakarsu ta zo karshe.

Advertisement

Sanarwar ta kuma ce wasikar ta kunshi bayanan da ke nuna cewa budurwar ta taba daukar ciki sau uku a lokacin da suke tare, lamarin da ya kara jefa ta cikin damuwa.

Sakamakon haka, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Anambra, Ikioye Orutugu, ya bayar da umarnin mika binciken lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Awka domin gano cikakken abin da ya faru.

Advertisement

Orutugu ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara su kara sanya ido kan halaye da mu’amalar ’ya’yansu, tare da ba su kulawar da ta dace domin kauce wa fadawa cikin matsalolin rayuwa da ka iya jefa su cikin halin kunci.

Haka kuma ya bukaci shugabannin gargajiya, malamai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tarbiyya su hada kai wajen wayar da kan matasa kan muhimmancin neman shawara da tallafi a lokutan da suke fuskantar kalubale. Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike tare da daukar matakan da suka dace kan lamarin.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending