News
Yansandan Jihohi Za Su Mayar da Najeriya Baya Zuwa Matsalolin Shekarun 1960 — Tsohon Kwamishinan ‘Yansanda

Tsohon Kwamishinan ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Wakili, wanda aka fi sani da CP Singham, ya yi gargadin cewa kafa rundunar ‘yan sandan jihohi na iya mayar da Najeriya cikin irin matsalolin siyasa da na tsaro da ƙasar ta fuskanta a shekarun 1960.
Wakili ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Jaridar Daily Trust, inda ya ce har yanzu bai ga wata hujja mai gamsarwa da za ta tabbatar da cewa kafa ‘yan sandan jihohi ita ce mafita ga matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta ba.
Mutane 8 Sun Mutu, 17 Sun Jikkata A Mummunan Hatsarin Mota A Katsina
A cewarsa, kafa irin wannan runduna na iya bai wa gwamnoni damar amfani da ita wajen cimma muradun siyasa, lamarin da ka iya haifar da cin zarafin doka da tauye adalci.
Ya ce maimakon ƙirƙirar sabuwar rundunar ‘yan sanda, ya kamata gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen sake fasalin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, ta hanyar inganta horo, samar da isassun kayan aiki na zamani, ƙara yawan jami’ai, da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da aikinta.
Tsohon kwamishinan ya kuma jaddada cewa kasancewar rundunar ‘yan sanda ƙarƙashin tsari guda a faɗin ƙasa na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa haɗin gwiwar jami’an tsaro, yaƙi da aikata laifuffuka da kuma tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.
Kalaman Wakili na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan kudirin kafa ‘yan sandan jihohi, inda masu goyon bayan shirin ke cewa zai taimaka wajen kusantar jami’an tsaro da al’umma tare da inganta tsaro. Sai dai masu adawa da kudirin na nuna fargabar cewa rundunar na iya zama kayan aikin siyasa a hannun gwamnonin jihohi.
