Connect with us

News

Rundunar Sojin Najeriya Ta Ayyana Neman  Jami’inta Ruwa A Jallo Kan Zargin Taimaka Wa ‘Yan Ta’adda

Published

on

wanted 1024x597 (1)

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana wani jami’inta, Private Mohammed Yusuf Amutu, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin sayar wa ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka kayan aikin soja.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce binciken farko ya nuna cewa jami’in, wanda ke aiki a Nigerian Army Ordnance Kits Factory, ya tsere daga sansaninsa tun ranar 3 ga Yunin 2026, kuma tun daga lokacin ba a san inda yake ba.

Aƙalla Fasinjoji 68 Ne Suka Tsallake Rijiya Da Baya A Jirgin Enugu Air

Sanarwar ta bayyana cewa ana neman jami’in ne domin ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa na sayar da kayan aikin soja ga masu aikata laifuka.

Rundunar ta ce ba za ta yi sassauci da duk wani jami’in da zai yi amfani da aikinsa wajen taimaka wa ‘yan ta’adda ko wasu masu aikata laifuka ba. Ta jaddada cewa duk wanda aka samu da hannu a irin wannan laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani bisa dokokin soja da na kasa.

Har ila yau, rundunar ta yi kira ga al’umma da su bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan da za su taimaka wajen gano inda jami’in yake domin ci gaba da bincike.

Advertisement

Ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace wajen kare tsaron kasa da kuma tabbatar da mutuncin Rundunar Sojin Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending