Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyyar mutuwar Mutane 107 Tare Da Jikkata 344 A Pakistan

Published

on

afp 6a66d8ffefe0 1785125120 (1)

Mamakon ruwan sama da ambaliya ruwa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 107 da jikkata wasu 344, tare kuma da lalata ɗaruruwan gidaje tun daga ƙarshen watan Yuni zuwa yau a Pakistan.

Hukumar Kiyaye Afkuwar Iftila’i ta ƙasar NDMA, ta shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon mamakon ruwan saman tun daga ƙarshen watan Yuni sun kai 107.

Gwamnatin Bauchi Ta Musanta Rahoton Kayyade Sadakin Budurwa zuwa ₦3,000 Da Na Bazawara Zuwa ₦1,500

Adadin mutanen da su ka rasu a lardin Khyber Pakhtunkhwa ya kai 55, tare da mutane 36 a yankin Punjabi. Kuma fiye da rabin mutanen sun mutu ne sakamakon rushewar gidajen da su ke ciki.

Jaridar ALJAZEERA ta ruwaito cewa hukumomin ƙasar sun samar da sansanoni guda 17 a birnin Lahore, domin zaunar da mutanen da su ka rasa muhallansu a sakamakon iftila’in.

Babbar Ministar Punjabi, Maryam Nawaz Sharif, ta bayyana cewa tuni hukumomin bayar da agajin gaggawa su ka bazama a dukkan yankunan domin gudanar da ayyukansu.

Advertisement

Inda hukumomin ƙasar su ka buƙaci al’ummar yankunan da su ci gaba da yin takatsantsan dangane da wuraren da za su shiga.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending