Connect with us

News

‘Yan Bindiga Sun Nemi Naira Miliyan 200 Kuɗin Fansa Domin Sakin Alƙalin Babbar Kotun Kebbi

Published

on

6a66f1a3dd465ae36b6 750x518

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun nemi Naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansa domin sakin Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza, wanda aka yi garkuwa da shi a jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, CP Umar Muhammad Hadejia, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Litinin a Birnin Kebbi.

Zargin Satar Waya Ya Jawo Mutuwar Matashi A Jos

A cewarsa, an yi garkuwa da Mai Shari’a Bunza ne da sanyin safiyar ranar Lahadi daga gidansa da ke kan titin Zogirma a Ƙaramar Hukumar Bunza.

Ya ce bayan samun rahoton lamarin, rundunar ta tura haɗaɗɗun jami’an tsaro zuwa yankin domin fara bincike da kuma neman ceto alƙalin.

Hadejia ya ce binciken farko ya nuna cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalan alƙalin tare da neman a biya su Naira miliyan 200 kafin su sake shi.

Advertisement

Ya ƙara da cewa an baza jami’an tsaro a hanyoyin da ake kyautata zaton maharan suka bi, tare da kafa shingayen bincike domin hana su tserewa.

Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ganin an ceto Mai Shari’a Bunza cikin ƙoshin lafiya, tare da cafke waɗanda suka aikata laifin.

 

 

LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending