Connect with us

News

NAPTIP Ta Ceto Mutane 258 A Jigawa

Published

on

NAPTIP

Hukumar Yaƙi da Fataucin Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) reshen Jihar Jigawa ta ce ta ceto mutane 258 tare da haɗa su da iyalansu tun bayan kafa ofishinta a jihar, yayin da ta bayyana cewa fataucin bil adama na ci gaba da zama babbar barazana ga al’umma.

Kwamandan hukumar a Jigawa, Abdulkadir Mahmoud Turajo, ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar domin bikin Ranar Yaƙi da Fataucin Bil Adama ta Duniya ta shekarar 2026, wadda ake gudanarwa a ranar 30 ga watan Yuli na kowace shekara.

INEC: ’Yan Sanda Su Ne Ya Kamata Su Jagoranci Ba Da Tsaro Lokacin Zaɓe, Ba Sojoji Ba

Ya ce Jigawa na daga cikin jihohin da masu fataucin mutane ke amfani da su a matsayin hanyar safarar mutane zuwa ƙasashen Turai da Gabas ta Tsakiya, ta hanyar Jamhuriyar Nijar, da kuma ta Chadi da Sudan zuwa Saudiyya.

Turajo ya bayyana cewa taken bikin na bana shi ne “An Daƙile Tarkon Damfara”, domin wayar da kan jama’a kan yadda masu fataucin mutane ke amfani da tallace-tallacen ayyukan bogi, damfarar intanet da sauran dabarun yaudara wajen jefa mutane cikin tarkonsu.

A cewarsa, fataucin bil adama wata irin bautar zamani ce da ta haɗa da ɗauka, jigilar mutane, saye da sayarwa ko ɓoye su ta hanyar yaudara, barazana ko tilastawa domin cin moriyarsu ta hanyar aikin dole, lalata da mata da yara, da sauran nau’o’in cin zarafi.

Advertisement

Ya ƙara da cewa wannan laifi na da alaƙa da wasu manyan laifuka da suka haɗa da cin hanci da rashawa, ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, safarar miyagun ƙwayoyi, garkuwa da mutane, ta’addanci da kuma halasta kuɗaɗen haram.

Kwamandan ya ce tun bayan kafa ofishin NAPTIP a Jigawa a watan Yulin 2023, hukumar ta yi rajistar shari’o’in fataucin bil adama guda 78, ta ceto mutane 258, sannan ta samu hukuncin ɗaurin masu laifi biyu, ciki har da wani ɗan ƙasar waje.

Haka kuma ya bayyana cewa tsakanin watan Janairun 2025 zuwa Yulin 2026, ƙungiyar International Organization for Migration (IOM) ta taimaka wajen dawo da ‘yan asalin Jigawa 512 daga ƙasashe daban-daban bayan sun shiga halin ƙaura ko kuma suka faɗa hannun masu fataucin mutane.

Turajo ya yi kira ga iyaye, matasa da shugabannin al’umma da su kasance masu taka-tsantsan, tare da gaggauta kai rahoton duk wani motsi ko alamar da ake zargin tana da alaƙa da fataucin bil adama domin kare rayuka da makomar al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending