Sports
Kasuwar ‘yan ƙwallo: Makomar Nunez, Jorginho, Tchouameni, Azpilicueta, Phillips
Newcastle ta gabatarwa Benfica tayin euro miliyan 60 (£50m) kan ɗan wasan Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 22, a kokarin shan gaban ƙungiyoyin Firmiya da ke farautarsa. (Footmercato – in French)
Mai horarwa Maurizio Sarri ya matsu ya sake aiki da Jorginho a Lazio, yayinda alamomi ke nuna da wuya a sabunta kwantiraginsa a Chelsea da zai zarta 2023. (90min)
Sabon kocin Manchester United Erik ten Hag na son dauko ɗan wasan Monaco Aurelien Tchouameni mai shekara 22. (ESPN)
Arsenal na nuna zawarcinta kan ɗan wasan Hoffenheim Florian Grillitsch, mai shekara 26 a wannan kakar. (Telegraph, via Metro) ko
Leeds United ta bi sahun Arsenal da Newcastle United a farautar ɗan wasan nan Grillitsch. (Mail)
Mai buga tsakiya a Ingila Kalvin Phillips, na son ci gaba da zama a Leeds kuma zai yi watsi da tayin da Manchester Unitedke yi masa. (Sun)
Tottenham ta shiga kasuwar lalauben ‘yan wasan gefe da tsakiya a wannan kakar, kuma da alama ta na sanya ido kan ɗan wasan Sifaniya Mario Hermoso daga Atletico Madrid. (Mail)
Borussia Dortmund ta kai wani matsayin a kokarin daidaitawa da Red Bull Salzburg kan ɗan wasa Karim Adeyemi, sai dai ɗan wasan gaban asalin Jamus na kuma tattaunawa da Liverpool, RB Leipzig da Paris St-Germain. (Sky Sport Germany – in German)
Zabin Chelsea na biyu wato mai tsaron raga a Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 27, ya ja hankalin Juventus. (Fichajes – in Spanish)
Tottenham na da kwarin-gwiwar daidaitawa da ɗan wasan West Bromwich Albion mai tsaron raga Sam Johnstone, duk da cewa ana harinsa a Manchester United. (Express)
Barcelona ta zage dantse a farautar kyeftin ɗin Chelsea Cesar Azpilicueta, mai shekara 32, da ke son barin Stamford Bridge saboda matsalolin da kulob din ke ciki. (Sport – in Spanish)
Paolo Dybala mai shekara 28, na shirin ganawa da Arsenal da Tottenham yayinda kwantiragin ɗan wasan na Argetina ke karewa a Juventus.(Express, via Corriere Dello Sport)
Kungiyoyin Turai da Firimiya sun mika tayinsu kan dan wasan TorinoGleison Bremer, su Arsenal, Leicester, Everton da Newcastle duk sun tuntubi kungiyar ta Serie A. Tottenham da Atletico Madrid duk sun aike tayi, haka zalika Bayern Munich da Borussia Dortmund na sa wa ɗan wasan mai shekara 25 ido. (Gazzetta Dello Sport – in Italian)
Ɗan wasan Belgium Eden Hazard, baya son barin Real Madrid a wannan kakar, duk kuwa da cewa yana samun tayi daga Arsenal, AC Milan da Borussia Dortmund. (RTBF, via RTL Sport – in French)
Manchester City na cigaba da matsa kaimi kan Erling Braut Haaland. (90min)
Ɗan wasan Arsenal Gabriel Magalhaes mai shekara 24, ya ce yana jindadin zamansa a Emirates, yayinda ake radi-radin cewa zai tafi Barcelona. (Fabrizio Romano)
Fenerbahce da Galatasaray na son saye ɗan wasa Al RayyanJames Rodriguez, sai dai ɗan wasan ya wkadaitu da Atletico Madrid. (FotoMac, via Mundo Deportivo – in Spanish)
