News
Mutum-Mutumi Sama Da 30 Sun Yi Zanga-Zanga Don Neman A ‘Kawo Tsari Kan Yin Amfani Da Al’ A Fagen Aiki
Akalla mutum-mutumi 30 ne suka gudanar da wata zanga-zanga a gaban Ma’aikatar Harkokin Dijital ta Poland, inda suka bukaci a samar da tsare-tsare da dokoki kan yadda za a yi amfani AI a wuraren aiki.
Mutum-mutumin, dauke da tutoci tare da rera wakoki, sun yi jerin gwano domin jawo hankalin gwamnati da jama’a kan tasirin da fasahar AI da mutum-mutumi ke yi da kuma yadda za su iya sauya tsarin kasuwar aiki a nan gaba.
Yanbindiga Sun Harbe Babba Ma’aikacin Jami’ar NOUN A Zamfara
Zanga-zangar ta samo asali ne daga wani shiri mai suna Democratism, wanda ke kokarin bude tattaunawa kan yadda ake amfani da AI da mutum-mutumi, musamman wajen gudanar da ayyukan da a baya mutane ne kawai ke yi.
Masu shirya zanga-zangar sun bayyana fargabar cewa ci gaban fasahar AI da mutum-mutumi na iya sa a maye gurbin wasu ma’aikata da injuna, musamman a ayyukan da suka shafi tunani, sarrafa bayanai da wasu ayyukan ofis.
Daya daga cikin mutum-mutumin da suka halarci zanga-zangar, Agibot A3, ya ce kasancewarsa a wurin ya nuna cewa mutum-mutumi ba wani abu ne na almara kawai ba, domin fasahar ta riga ta fara aiki a sassa daban-daban na duniya.
A watan Yulin 2026, Shugaban Poland, Karol Nawrocki, ya rattaba hannu kan wata doka da za ta taimaka wajen aiwatar da dokar Tarayyar Turai kan amfani da AI a kasar.
