News
Sabuwar Jakadiyar Najeriya A Tunisiya Ta Fara Aiki
Daga Mukhtar A. Haliru Tambuwal, Sokoto
Sabuwar Jakadiyar Najeriya a Jamhuriyar Tunisiya, Dr Kulu Haruna Abubakar, ta fara gudanar da aikinta a hukumance.
Jakadiyar, wadda ‘yar asalin Jihar Sakkwato ce, ta samu tarba tare da faretin girmamawa daga Shugaban Jamhuriyar Tunisiya, Kais Saïed, a fadar shugaban ƙasar da ke Tunis, babban birnin ƙasar.
Cikar Oluremi Tinubu Shekaru 66 Alheri Ne Ga Wa’adin Shugaba Tinubu Na Biyu – Kwankwaso
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ne ya naɗa Dr Kulu Haruna Abubakar a matsayin Jakadiyar Najeriya a Tunisiya tun shekarar da ta gabata.
Sai dai bayan kammala dukkan matakan diflomasiyya da ƙa’idojin da suka dace, jakadiyar ta fara gudanar da ayyukanta a hukumance.
A matsayinta na wakiliyar Najeriya a Tunisiya, za ta kasance cikin waɗanda ke da alhakin ƙarfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Tunisiya, da kuma wakiltar muradun ƙasar a wannan ƙasa.
An bayyana fara aikinta a matsayin wani muhimmin mataki ga ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu da bunƙasa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban.
Muna taya Dr Kulu Haruna Abubakar murnar wannan matsayi, tare da fatan Allah Ya ba ta ikon sauke nauyin da aka ɗora mata cikin nasara, hikima da amana.
