Uncategorized
APC Ta Sasanta Rikicin Cikin Gida A Kano Ta Kudu, Ta Haɗa Kai Don Tabbatar Da Nasarar Tinubu, Abba, Doguwa Da Sauransu
Daga Muhammad Kabir, Kano
Jam’iyyar APC a yankin Kano ta Kudu ta samu nasarar sasanta rikicin cikin gida da ke tsakaninta da wasu mambobinta, yayin da ‘yan jam’iyyar suka amince su haɗa kai domin tunkarar zaɓen 2027.
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Tudun Wada/Doguwa, Alhassan Ado Doguwa, ne ya bayyana hakan yayin rabon tallafin naira miliyan 25 ga magoya bayan APC a mazaɓu uku na Ƙaramar Hukumar Tudun Wada.
KASSTOWA Ta Ƙara Jami’an Tsaro A Wajen Samar Da Ruwa Na Joda
Doguwa ya ce Shugabar Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON) a Kano, Sa’adatu Salisu Soja, da mijinta, Salisu Yushau Soja, tare da sauran masu ruwa da tsaki a yankin, sun ajiye saɓanin da ke tsakaninsu domin haɗa kai don ganin APC ta samu nasara.
Ya ce sulhun ya nuna cewa ‘yan APC a Kano ta Kudu sun fahimci muhimmancin haɗin kai, musamman yayin da jam’iyyar ke shirin tunkarar zaɓukan 2027.
A cewarsa, haɗin kan zai taimaka wajen tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa, Murtala Sule Garo, da kuma ‘yan takarar jam’iyyar a majalisun dattawa, wakilai da na dokokin jiha.
Doguwa, wanda ke neman sake komawa Majalisar Wakilai, ya bayyana hakan ne yayin da yake raba taraktocin noma guda 10, naira miliyan 25, injinan ɗinki, babura da motoci ga magoya bayan APC a yankin.
Ya kuma yi gargaɗin cewa bai kamata wani ya yi ƙoƙarin kawo cikas ga sulhun da aka cimma ba, yana mai cewa rikicin cikin gida na iya kawo wa jam’iyya cikas wajen cimma manufofinta na siyasa.
Da yake jawabi a wajen taron, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa ya ce Kano ta Kudu ba ta taɓa samun irin wannan haɗin kai da sulhu tsakanin ‘yan siyasa ba.
Ya bayyana hakan a matsayin wata alama da ke nuna cewa APC na da damar samun nasara a zaɓukan 2027, yana mai cewa rashin jituwa da rikicin cikin gida na kawo cikas ga ci gaban jam’iyya da aiwatar da ayyukan more rayuwa.
Shi ma Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa rawar da ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mambobin APC a jihar.
Garo ya ce matakin da gwamnan ya ɗauka na sasanta ‘yan jam’iyyar ya nuna dattaku, balaga da tsoron Allah.
A nasu ɓangaren, al’ummar Tudun Wada da Doguwa sun nuna godiya bisa tallafin da suka samu, tare da alƙawarin yin amfani da kayan tallafin wajen inganta rayuwar iyalansu da al’ummominsu.

