Connect with us

News

IAR ta samar da gajerun irin dawa domin taimaka wa manoma a yankunan da ke fama da matsalar tsaro

Published

on

IMG 20261108 WA0000
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Cibiyar Binciken Harkokin Noma (IAR) da ke Samaru, a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ta samar da sabbin nau’ikan irin dawa masu saurin nuna amfanin gona, domin taimaka wa manoma a yankunan da ke fama da matsalar tsaro da kuma sauyin yanayi a Najeriya.

Dakta Muhammad Ahmad Yahaya, wanda ke jagorantar binciken inganta sabbin nau’ikan dawa a cibiyar, ne ya bayyana hakan yayin wani taron baje kolin amfanin gona (Field Day) da aka gudanar a gonar binciken IAR da ke Samaru, domin nuna wa manoma sabbin nau’ikan irin da cibiyar ta samar.

KANO: Kwamitin Yaƙi Da Shaye-shaye Ya Ƙwato Kwayoyin Pregabalin Miliyan 3.18

Ya ce cibiyar ta yi la’akari da manyan ƙalubalen da manoma ke fuskanta, musamman sauyin yanayi da matsalar tsaro da ta addabi wasu yankunan Arewacin Najeriya, wajen samar da irin da zai dace da halin da ake ciki.

A cewarsa, Hukumar Raya Ƙasashen Duniya ta Birtaniya (FCDO) ce ta bayar da tallafin gudanar da aikin binciken, da nufin samar da ingantattun irin dawa ga al’ummomin da ke fama da ƙarancin samun iri mai inganci, domin ƙara samar da abinci.

Dakta Yahaya ya bayyana cewa sabbin nau’ikan da aka samar sun haɗa da SAMSORG 52, SAMSORG 53 da SAMSORG 54, waɗanda tuni aka fitar domin manoma su fara amfani da su.

Advertisement

Ya ƙara da cewa samar da irin da ke saurin nuna amfanin gona zai taimaka wajen rage haɗarin da manoma ke fuskanta sakamakon rashin tsaro da kuma sauyin yanayi, musamman a wuraren da ba a samun damar yin noma na tsawon lokaci.

A nata ɓangaren, ɗaya daga cikin manoman da suka halarci taron, Uwale Balarabe, ta ce ta shafe sama da shekaru 15 tana aikin noma, amma ba ta taɓa samun damar halartar irin wannan taro ba.

Ta bayyana farin cikinta da ganin sabbin nau’ikan dawa da aka samar, tana mai cewa tana fatan yin amfani da su saboda yadda aka inganta su domin su dace da ƙalubalen tsaro da sauyin yanayi da manoma ke fuskanta a yanzu.

Shi ma Sarkin Bumu, Alhaji Muktar Usman, wanda ya halarci taron, ya bayyana samar da sabbin irin dawar a matsayin wani gagarumin ci gaba da ya zo a lokacin da ake matuƙar buƙatarsa.

Ya ce: “Haƙiƙa an yi tunani sosai wajen samar da waɗannan irin dawa, domin suna iya nuna amfanin gona cikin ƙasa da watanni huɗu. Wannan ya bambanta da tsofaffin irin da ake nomawa, waɗanda suke ɗaukar kusan dukkan lokacin damina kafin su nuna.”

Alhaji Muktar ya ce irin wannan yunƙuri zai taimaka wajen bunƙasa harkokin noma da inganta samar da abinci, musamman ga al’ummomin da matsalar tsaro ke hana su gudanar da noma yadda ya kamata.

Advertisement

Ya kuma yabawa cibiyar IAR bisa wannan ƙoƙari, yana mai cewa samar da irin da ya dace da yanayin da ake ciki wata muhimmiyar hanya ce ta tallafa wa manoma da ƙarfafa samar da abinci a ƙasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending