News
’Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motocin Buhari Hari A Hanyar Daura
Daga kabiru basiru fulatan
’Yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Yammacin Talatar nan a hanyarsu ta zuwa garin Daura da ke Jihar Katsina.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mallam Garba Shehu ya fitar, ta ce ’yan bindigar sun kai hari kan ayarin motocin ne dauke da jami’an tsaro da sauran hadimai a shirye-shiryen da shugaban kasar ke yi na tafiya Daura domin bikin Babbar Sallah.
ALLAH ƊAYA GARI BAMBAN:Magajin-gari ya auri kada a Mexico
Malam Shehu ya ce ’yan bindigar da suka yi wa ayarin motocin kwanton bauna, sun fuskanci tirjiya daga jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ’yan sanda da kuma DSS wadanda suka mayar musu da martani.
Sanarwar ta ce biyu daga cikin ya tawagar na karbar magani a sakamakon wasu kananan raunuka da suka samu, inda dukkan sauran ma’aikata da hadiman shugaban kasar suka isa Daura cikin aminci.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News7 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
