Connect with us

News

Kare ya ɗauki rainon marayun ƴaƴan agwagwa 15 bayan mahaifiyarsu ta ɓata

Published

on

Daga Maryam bashir musa 

 

 

 

A wani yanayi na tausayi da jin-ƙai, wani kare mai ban sha’awa, mai suna Fred, ya ɗauki rainon wasu marayun ƴaƴan agwagwa 15, bayan mahaifiyarsu ta ɓace ba zato ba tsammani.

Wani rahoto da jaridar Daily Mirror ta fitar ya baiyana cewa Fred, mai shekaru 15, ya yi suna wajen rainon dabbobi ƴan’uwansa.

Advertisement

’Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motocin Buhari Hari A Hanyar Daura

A 2018, Fred ya game kafafen yaɗa labarai bayan da ya raini was marayun ƴaƴan agwagi guda tara da aka watsar a cikin irin wannan yanayi.

Shekaru bayan nan, tsohon karen ya kasance baya-goya-marayu ga ƴan’uwansa karnuka.

Wasu hotuna da su ka kewaye kafafen sadarwa sun nuna ƙananan ƴaƴan agwagin a durƙushe a tsakanin kafafun Fred, inda wasu kuma su ka ɗare bayansa cikin wani yanayi na shaƙatawa, yayin da suke kwance tare a rana.

Ƴaƴan agwagin, masu launin ɗorawa, hotonsu ya bayyana inda su ke kwance a bayan Fred wanda shi ne sabon uba a gare su.

Fred mazaunin Mountfitchet Castle ne kusa da Stansted, Essex, inda mahaifiyar ƴaƴan agwagin ta ɓace cikin dare.

Advertisement

Tun daga wannan lokacin, Fred ya ɗauki gaɓaren kula da su inda ya saɓa su a bayansa yana ɗauke da su a bayansa yana nuna su ga ma’aikata da baƙi.

Mai Fred, Jeremy Goldsmith, wanda kuma shi ne darekta na Dutsen Mountfitchet, ya ce bai yi mamakin cewa Fred ya sami sabbin ƴaƴa ba.

“A cikin shekaru 15 na mallakarsa, Fred ya shafe lokaci mai tsawo a Gidan tare da dabbobi kuma ya zama yanayi na biyu a gare shi kasancewa cikin dabbobin da aka ceto,” kamar yadda ya shaida wa Daily Mirror.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending