Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Harbe Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda A Katsina

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

’Yan bindiga sun harbe wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, Aminu Umar a Jihar Katsina.

Bayanai sun ce an ’yan bindigar sun yi wa mataimakin kwamishinan ’yan sandan da tawagarsa kwanton bauna ne a lokacin da suke sintiri a dajin Zakka da ke Karamar Hukumar Safana ta jihar.

Advertisement

 

Wakilinmu ya ruwaito cewa, gabanin rasuwarsa, Aminu Umar shi ne kwamandan rundunar ’yan sanda na yankin Dutsinma.

Majiyoyi a yankin na Zakka sun shaida wa Aminiya cewa, ’yan sanda da ’yan bindiga sun yi arangamar ce a wani kauye mai suna Yauni da ke gundumar Zakka a cikin garin Safana.

Da yake tsokaci kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce Umar ya mutu ne a karon-battar da ’yan sanda suka yi da ’yan bindiga sama da 300.

Ya ce akwai kuma karin wani ya riga mu gidan gaskiya a sakamakon artabun, sai dai bai bayyana ko wane ne dayan da ajali ya katse wa hanzari ba.

 

Advertisement

Source Aminiya 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending