Sports
Dan wasan gaban Chelsea Romelu Lukaku ya ce ba ya jin dadin zamansa a Chelsea kuma akwai yiwuwar ya sake komawa wurin tsohon kocinsa Antonio Conte, Tottenham
Muhammad zahraddin
Dembele da dan wasan gaban Manchester United Anthony Martial. (Ara – in Catalan)
Kungiyoyin Manchester United da Manchester City da Chelsea na rububin sayen dan wasan tsakiyar West Ham Declan Rice. (Sun)
Newcastle na son sayen yan wasa shida kafin a rufe kasuwa, da suka hada da Kieran Trippier na Atletico Madrid kafin haduwarsu da Watford ranar 15 ga Janairu. (The I)
Tottenham da West Ham na daga cikin kungiyoyin da ke takarar sayen Adama Traore, wanda Wolves ta shirya sayarwa kan fam miliyan 20 don ta samu kudin sayen wasu yan wasa. (Telegraph – subscription required)
Jaridar(Calciomercato – in Italian) kuwa ta ruwaito cewa Liverpool da AC Milan na son sayen dan wasan tsakiyar Guinea da ke wasa a Olympiakos Aguibou Camara.
Aston Villa na daga kungiyoyin baya bayan nan da ke sha’awar sayen Denis Zakaria da ke buga tsakiya a Borussia Monchengladbach a Jamus.(Mail)
Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce za su bari sai karshen kaka, kafin su yi kokarin kulla yarjejeniya da Kylian Mbappe na PSG.(Goal)
Shi kuwa mai tsaron ragar Barcelona Neto ya fada wa kulob din cewa yana so ya kara gaba zuwa Flamengo da ta nuna sha’awar sayensa. (El Nacional – in Catalan) AC Milan kuwa na duba yiwuwar neman dan wasan gaban Torino Andrea Belotti, wanda zai iya barin kungiyar idan kwantiraginsa ya kare a karshen kaka. (Calciomercato – in Italian)
