News
Takarar shugaban ƙasa a APC: Ba wanda ya gagara na kara da shi — Orji Kalu
Daga kabiru basiru fulatan
Bulaliyar Majalisar Dattijai, Orji Kalu ya ce a shirye ya ke ya tsaya takarar shugaban ƙasa idan Jam’iya mai Mulki ta APC ta kai takarar ɓangaren kudancin ƙasar nan.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa Jagoran APC na Ƙasa, Bola Tinubu ya sahidawa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari aniyar sa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar nan af jam’iyar a 2023.
Shima Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi da sauran ƴan jam’iyyar sun baiyana aniyar su ta tsayawa takarar.
A wata sanarwar da aya fitar a yau Laraba, tsohon gwamnan Jihar Abia ya ce duk da cewa ba ya adawa da neman takarar kowa, ya amince cewa ya kamata a kai takarar shugaban ƙasa zuwa yankin Kudu-maso-Gabas.
Ya jadda cewa in dai Kudu-maso-Gabas za a kai takarar shugabancin kasa, to shine zai tsaya takarar.
A cewa Kalu yana da duk abinda wani ya ke ji da shi kuma ba wanda ya gagara ya kara da shi a neman tikitin takarar shugaban ƙasa a APC.