News
Jihar Ebonyi ba za ta taɓa shiga Biafra ba – Gwamna David Umahi
Daga muhammad muhammad zahraddin
Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya ya bayyana cewa jiharsa “ba za ta taɓa shiga yunƙurin kafa ƙasar Biafra ba”.
Kazalika gwamnan ya roƙi hukumomin Najeriya da su murƙushe duk wanda ke son tayar da hankali a yankinsu na kudu maso gabas.
Umahi wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC mai mulki, ya faɗi hakan ne a Abakaliki babban birnin jihar ranar Alhamis yayin wata liyafa da aka haɗa masa.
“Abu na farko dai, na sha faɗa, duk wanda ya tambaye ku game da Biafra ku ce Ebonyi ba za ta taɓa shiga Biafra ba. Mu ba ‘yan Biafra ba ne,” in ji shi.
“An wulaƙanta mu (a baya) kuma yanzu ne muke wartsakewa amma kuna so mu koma baya. Ba za mu koma ba.
“Na faɗa wa gwamnonin yankin kudu maso gabas cewa mu muna son mafita ne ta hanyar siyasa sannan kuma duk wanda yake son tayar da hankali a murƙushe shi.”
Ana yawan samun tashin hankali a yankin kudu maso gabashin Najeriya inda ƙabilar Igbo ke da rinjaye sakamakon ayyukan ƙungiyoin da ke son kafa ƙasar Biafra mai cin gashin kanta.
“Babu wani ɗan ƙabilar Igbo da zai zama shugaban ƙasa kuma ba zai so ɗorewar Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya ba, saboda muna da dukiya a ko’ina (a faɗin Najeriya),” in ji shi.