News
Kwamishinan Ƴan Sandan Borno ya tabbatar da harin Boko Haram kan Makarantar Horon Ƴan Sanda a Gwoza
Daga kabiru basiru fulatan
Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar Borno, Abdul Umar ya tabbatar da cewa da ƴan Boko Haram sun kai hari kan Makarantar Horon Ƴan Sanda a Gwoza.
Ya ce harin ya faru ne a jiya Alhamis, in da ya musanta cewa ƴan ta’addan sun yi garkuwa da wasu jami’an ƴan sanda.
Ya nuna cewa ƴan sandan nema su ka fatattaki ƴan ta’addan.
A yayin wani taron manema labarai a Maiduguri a yau Juma’a, Kwamishinan ya ce ‘hankalin Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Borno ya kai kan wani rahoto da ke yawo a kafafen sadarwa cewa an yi garkuwa da wasu jami’an mu a Makarantar Horon Ƴan Sanda a Gwoza.
“Rundunar mu na mai tabbatar da cewa wannan labarin ƙarya ne, sannan ina mai sanar da ku cewa ƴan sandan mu sun samu nasarar fatattakar ƴan ta’addan da su ka kai hari kan Makarantar a ranar 13 ga watan Janairu, 2022,”
Ya ƙara da cewa, “ba wani ɗan sanda da harin ya shafa, ko ƙwarzane ko rasa makami ba wanda ya yi.
“Ina so mai amfani da wannan dama na ja hankalin al’umma kan su dena yarda da labaran ƙarya da za su haifar da tsoro da fargaba a zukatan jama’a ya kuma gurɓata zaman lafiyar da jama’a ke ciki har su na harkokin su na yau da kullum, sannan ina mai jaddada musu cewa za mu ci gaba da kokari mu tabbatar an kawo ƙarshen rashin tsaro a Jihar Borno,” in ji Umar.