News
Gwamnatin Kano za ta kashe miliyan 500 don ƙawata gadar ƙasa ta Kurna
Daga muhammad muhammad zahraddin
Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta amince da ware naira miliyan 500 (N525, 435,750) don ƙawata gadar-ƙasa ta Tijjani Hashim da ke Kurna a ƙwaryar birnin.
Kwamashinan Yaɗa Labarai Muhammad Garba ne ya bayyana hakan bayan kammala zaman majalisar a ranar Alhamis, yana mai cewa za a ƙawata gadar da ƙananan duwatsu masu ƙyalli.
Ya ƙara da cewa an ɗauki matalkin ne don rage yawan kwararar shara cikin hanyar ta ƙasa.
Ya ce kazalika majalisar ta amince a sake ba da kwantiragi na saka duwatsu masu ƙyalli don ƙarfafa ginin bangon gadar ƙasa da ke Panshekara zuwa Madobi kan kuɗi naira miliyan 65 (N65, 709, 198).
Sauran ayyukan da gwamnatin Kano za ta yi sun haɗa da biyan kuɗin makaranta da alawus na ɗaliban jihar da gwamnati ta ɗauki nauyi a Indiya, inda aka ware naira miliyan 25 (N25, 559, 600).
Haka nan, an ware miliyan 32 don sauya jadawali da kuma ayyukan makarantun gwamnati zuwa na zamani a jihar, sannan za a kashe miliyan 19 wajen shirya wasanni na shekara-shekara da zimmar tunawa da tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya Murtala Ramat Muhammad.