Connect with us

News

Rikicin APC a Kano: Ganduje da Shekarau sun miƙa buƙatun su na kasafta muƙaman jam’iya ga kwamitin sulhu

Published

on

FB IMG 16440399609266124
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

A jiya Juma’a ne dai kwamitin sulhun rikicin jam’iyar APC a Kano, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Riƙon Ƙwarya na APC na Ƙasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sake zaman sulhunta tsakanin ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a zaman da a ka yi na ranar Talatar da ta gabata, Ganduje bai halarta ba bai kuma tura wakili ba.

Majiyoyi sun ce gwamnan ya ƙi halartar zaman ne sabo da ya na da yaƙinin samun nasara a kotun ɗaukaka ƙara, bayan da wata Babbar Kotu a Abuja ta rushe shugabancin ɗan takarar sa na shugabancin jam’iya na jiha, Abdullahi Abbas.

Advertisement

Kwatsam kuma sai ga gwamnan a zaman na jiya Juma’a bayan da a ranar Alhamis, kwamitin riƙo na jam’iyar ya rantsar da shugabannin jam’iya na jiha na jihohi 34, amma ban da Kano da Sokoto.

A zaman sulhun dai na jiya, wanda a ka kwashe awanni shida a na gabzawa, ba a cimma matsaya ba.

Sai dai kuma kowanne ɓangare ya miƙa kundin buƙatarsa ta yadda ya kamata a kasafta muƙaman jam’iya ga shugaban kwamitin, Buni.

Advertisement

Kwamitin kuma zai yi nazari a kan buƙatun da kuma kasafta muƙaman, inda da ga bisani za a sake kiran zaman a shaidawa ɓangarori biyun irin kasafin muƙaman da kwamitin ya yi.

Amma wasu majiyoyi da su ke cikin zaman sulhun sun shaidawa Daily Nigerian Hausa cewa zai yi wuya duka ɓangarori biyun su amince da kasafin.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *