Connect with us

News

Gwamnatin Kano ta fara shirye-shiryen ƙara shekarun ritayar malaman makaranta

Published

on

FB IMG 16441637445077268
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamiti da zai yi garambawul na tsari da yanayin aikin malaman makaranta a jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar.

A sanarwar, Garba ya ce batun na ɗaya da ga cikin ƙudurirorin taron majalisar zartsawa.

Advertisement

Ya ce kwamitin zai zana jadawalin yin ritayar malamai na bai-ɗaya, wanda zai fara aiki da ga watan Janairun da ya gabata.

An umarci kwamitin, in ji Garba, da ya samar da wani tsari mai kyau da zai samar da nasarar sabon tsarin.

Kwamishinan ya ce sabuwar shekarun ritaya zai kasance da ga 35 zuwa 40 da kuma shekara 60 zuwa 64 na haihuwa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *