Majalisar Wakilan Najeriya ta nemi gwamnatin ƙasar ta dakatar da kamfanonin mai na ‘yan kasuwa da suka shigar da gurɓataccen man fetur ƙasar.
Ƙudirin da majalisar ta cimma a yau Alhamis wani ɓangare ne na binciken da wakilan ke yi game da asalin man, wanda ya lalata ababen hawan mutane da dama a faɗin Najeriya tun daga ƙarshen watan Janairu.
Tun farko shugaban kamfanin mai na gwamnatin Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya bayyana MRS da Oando da Duke Oil da Emadeb a matsayin kamfanonin da suka yi dakon man zuwa ƙasar daga Belgium.
NNPC ya ce yana ci gaba da bincike da kuma tuntuɓa don ɗaukar matakin da ya dace.
Ita ma hukumar kula da harkokin mai Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority (NMDPRA) ta ce ta gano matsalar kuma tuni ta dakatar da fitar da gurɓataccen man, wanda hakan ya haddasa dogayen layi a gidajen sayar da shi.