News
Kasuwar ‘yan ƙwallo: Makomar Kane, Haaland, Azpilicueta, Eze, Van de Beek, Gavi

Daga aminu usman jibrin
Harry Kane mai shekara 28 zai jinkirta zuwa karshen kaka kafin ya yanke matsaya kan makomarsa a Tottenham, ɗan wasan wanda shi ne kyeftin din Ingila ba shi da niyyar tsawaita kwantiraginsa a ƙungiyar. (Standard)
Real Madrid ta gabatar da tayin karshe kan ɗan wasan Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland mai shekara 21, wanda ka iya datse zawarcin Manchester United, Chelsea da Manchester City’s da ke saran saye ɗan wasan asalin Norway. (Sport, via Sun)
Arsenal ta tsinci kanta cikin kunci bayan gaza sayen ɗan wasan Serbia Dusan Vlahovic mai shekara 22, yayinda Mikel Arteta ke tsaka mai wuya kan laluben ‘yan wasa a sabuwar kaka. (Mirror)
Thomas Tuchel ya ce Cesar Azpilicueta ɗan wasa ne mai muhimmanci sosai har yanzu ga Chelsea duk da cewa kwantiragin ɗan wasan mai shekara 32 na gab da karewa. (Mail)
Barcelona ta gabatar da tayi kwantiragin shekara biyu da yiwuwar tsawaita shi kan ɗan wasan Chealse da take shirin rabo shi da Stamford Bridge wato Azpilicueta. (Fabrizio Romano, via Express)
Chelsea na cikin kungiyoyin da ke farautar ɗan wasan Barcelona da Sifaniya da ke buga tsakiya Gavi, mai shekara 17. (El Nacional)
Dan wasan baya a kungiyar Sevilla Jules Kounde mai shekara 23, na da damar komawa Chelsea idan ya bar kungiyar ta La Liga. (Fichajes – in Spanish)
Ɗan wasan Ingila Eberechi Eze na son ci gaba da zama a Crystal Palace yayinda ake jita-jita da alakanta shi da yunkurin komawa Newcastle. (Standard)
Wilfried Zaha na Crystal Palace na iya bankwana da kulob din a wannan kakar saboda da alama Eagles na son karban kudade kan matashin ɗan wasan mai shekara 29 kafin kwantiraginsa ya kare a 2023. (Mail)
Mai buga tsakiya a Dutch Donny van de Beek, mai shekara 24 na iya juyawa Manchester United baya domin samun gurbin din-dindin a Everton a wannan kakar idan ya taimaka musu a gasar firimiya yayin zaman aron da ya tafi. (Mirror)
Steven Bergwijn na Tottenham asalin Netherlands ya kasancewa wanda AC Milan ke farauta a yanzu. (Calciomercato)
Yunkurin komawar Andreas Pereira na Brazil Flamengona cikin barazanar rushewa, lamarin da ka iya sa Manchester United tafka asarar milyoyi. (Sport Witness, via Mirror)
Marcelo Bielsa yaƙi ya tattaunawa makomarsa yayin da ake rade-radin yiwuwar ya cigaba da zama a matsayin kocin Leeds. (Independent)