News
Gwamnatin Taraiya ta amince da kashe Naira Biliyan 2 domin sayen shanu a Taraba
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Ministar Jinƙai da Rage Raɗaɗin Ibtila’i da Ci gaban Al’umma ta Ƙasa, Sadiya Farouq ta baiyana cewa Majalisar Ƙoli ta ƙasa ta amince da fitar da kuɗi, wuri na gugar wuri har Naira Biliyan 2 domin sayen shanu don bunƙasa noman dabbobi a Jihar Taraba.
Da ta ke tattaunawa da manema labarai a fadar Shugaban Ƙasa a jiya Laraba, Ministar ta baiyana cewa tuni ma’aikatar ta ta aika da ƙunshin bayanan buƙatar ma’aikatar guda biyu.
Farouq ta ƙara da cewa ɗaya da ga ciki shi ne na neman sabunta kuɗin da za a kashe wajen sayo shanu a Taraba a karkashin Shirin Tallafin Gaggawa ga jihohin da su ka samu ibtila’in rigingimu da rashin tsaro.
Ministar ta ce ma’aikatar ta samu sahakewar kuɗaɗe da su ka kai naira biliyan biyu da ɗoriya.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
