News
Kamfanin Airtel ya ƙara ƙarfin sadarwar shi zuwa 4G a faɗin Nijeriya
Daga yasir sani abdullahi
Kamfanin Airtel a Nijeriya ya ce ya ƙara ƙarfin hanyar sadarwar shi a faɗin Nijeriya domin tabbatar wa da abokan hulɗar sa samun ingantacciyar hanyar yin kira da kuma data.
Shugaban kamfanin a nan Nijeriya, Surendran Chemmenkotil ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata a Jihar Legas.
Ya ce wannan aikin zai baiwa abokan hulɗar sa da su ka haura miliyan 50 damar yin kira da kuma amfani da data sama da kowanne kamfanin sadarwa a ƙasar.
Chemmenkotil ya yi bayanin cewa a aikin da a ka yi, Airtel ya ƙara ƙarfin hanyar sadarwar sa da ke kan matakin 2G da 3G zuwa 4G.
Ya ce yin hakan wani salo ne na daɗaɗa wa abokan hulɗar sa su samu damar yin kira ba tare da katsewa ba da kuma amfani da yanar gizo cikin sauri da sauki.
Ya kuma tabbatar da cewa Airtel zai ci gaba da goya wa gwamnatin Nijeriya baya wajen ƙudurin ta na faɗaɗa hanyar sadarwa a faɗin ƙasar.