Connect with us

Sports

Real Madrid ta tisa ƙeyar PSG gida

Published

on

Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

Real Madrid ta kora PSG gida a gasar zakarun turai cikin yanayin banmamaki.

Dab da tafiya hutun rabin lokaci ne Kylian Mbappe da ya ci Madrid daya a Paris ya kara jefa musu wata kwallo a minti na 39.

Advertisement

Dan wasan da bai fi shekara 23 ba ya zama na uku cikin wadanda suka fi jefa kwallo a matakin sili ‘yar kwale a gasar zakarun Turai inda yake biye wa Ronaldo da Messi.

Wannan kwallo ba ta kashe wa Real Madrid gwiwa ba sun ci gaba da kokari musamman bayan dawowa hutun rabin lokaci.

Cikin minti na 63 dan wasan Faransa Karem Benzema ya farke wa Madrid kwallon, ta hannun Vinicious.

Advertisement

Abin bai tsaya nan ba cikin minti na 76 dan wasan ya kara kwallo ta biyu a ragar PSG abin da ya fara kashe wa ‘yan wasan PSG gwiwa kenan.

Sai kwallo ta uku da dan wasan ya ci a minti na 78 minti biyu bayan cin kwallansa ta biyu, dan bayan PSG Marquinhos ne ya tafka wani kuskure abin da ya kai Benzema ya tsinci kwallo kuma ya jefata a raga.

PSG ta saba irin wannan rashin nasara a wasanninta, inda take iya samun nasara a karon farko a karshe kuma a fiddata.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *